An Samu Gawar Matar da ta Kama Daki Tare da Namiji a Legas

Manajan wani otal dake Igbogbo dake yankin Ikorodu a jihar a Legas ya tsinta gawar wata mata a daya daga cikin dakunan otal din a ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan yayin da ya zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Amurka.

Hundeyin yace manajan otal din ya kai korafin ofishin ‘yan sanda dake Ikorodu, jaridar The Nation ta rahoto.

Yace rahoton manajan ya bayyana cewa, matar mai shekaru 46 a duniya ta isa otal din a babur kirar Bajaj wacce wani Alfa Sule ya tuko a ranar Juma’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yace manajan ya bada rahoton cewa, Alfa Sule wanda ba a san daga inda yake ba, sun kama dakin tare da matar wacce daga bisani aka gano sunanta da Muinat.

An ga gawa amma namijin da suke tare yayi batan dabo
Hundeyin yace yayin da manajan ke zagaya dakunan a ranar Asabar wurin karfe 6 na safe, ya ga gawar matar amma Alfa Sule yayi batan dabo.

Leave a Comment