Atiku Ya Ziyarci Gombe, Ya Sha Alwashin Farfado da Madatsar Wutar Lantarki, Zai Habaka Kasuwanci

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi alkawarin tabbatar da wuta daga madatsar wuta ta Dadin Kowa da ke jihar Gombe idan aka zabe shi a zaben 2023, Guardian ta ruwaito.

A bangare guda, Atiku ya sissanta kansa da tsohon firayinministan Najeriya, marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, inda yace ‘yan Arewa maso Gabas za su samu alheri idan suka zabe shi a 2023.

Da yake magana a taron gangamin kamfen na PDP a jihar, Atiku ya ce dukkan hanyoyin da ke hada Gombe da Adamawa da Borno, da kuma hanyar da ke hada Gombe da Bauchi da Yobe duk za iyi aikin gyara su.

Ya ce za iyi hakan ne don habaka alakar kasuwanci tsakanin jihohin na Arewa naso Gabashin Najeriya, jaridar Independent ta ruwaito.

A cewarsa:

“Bari na maimaita alkawarin da na dauka idan Allah ya sa kun goyi bayan PDP. Mun yi alkawarin karfafa ‘yan kasuwanku don inganta kasuwanci ta yadda za su fadada kasuwancinsu don matasanmu maza da mata.

“Mun kuma yi alakawarin cewa, madatsar ruwan Dadin Kowa, wanda aka gina a mulkin PDP don samar da wutar lantarki da harkar noman rani za su fara aikin samar da wuta da noman rani matukar kuka goyi bayan gwamnatin PDP.”
“Za mu tabbatar dukkan hanyoyin da ke hada Gombe da Adamawa da Borno da Bauchi da Yobe duk an gyara su son habaka alakar kasuwanci.

“Da yawanku ba a haife ku ba lokacin da marigayi firayinminista Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi Mulki ba. Yanzu kuna da damar samun wani Abubakar Tafawa Balewan daga gare ni.”
A nasa bangaren, shugaban kwamitin gangamin PDP, kuma gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel y ace, tattalin arzikin zai dawo yadda yake a da kuma darajar Naira zai habaka idan aka zabi Atiku.

Leave a Comment