Ganduje Ya Shiga Tsakanin Rigimar Doguwa da Garo, Yayi Musu Sasanci

Kano – Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi sasanci tsakanin ‘yan jam’iyyar APC kan rikicin da ya hautsine a reshen jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Rikici ya barke a makon da ya gabata tsakanin shugaban masu rinjaye, wanda ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a tarayya, Alhassan Doguwa da ‘dan takarar mataimakin Gwamnan APC, Murtala Garo.

Doguwa a ranar Litinin ya tabbatar da cewa an sasanta su ga manema labarai a wani shirin gidan rediyon Kano.

An zargi Doguwa da jifan Garo da kofin shayi a yayin taron masu ruwa da tsaki a gidan mataimakin Gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, wanda hakan ya raunata kwamishinan kananan hukumomi da lamurran masarautu.

Shugaban masu rinjayen wanda ya musanta zargin da ake masa, ya sha alwashin cigaba da yakar Garo har zuwa karshe.

Sai dai a shirin gidan rediyon, Doguwa yace Gwamna Ganduje ya jagoranci sasanci inda yayi kiran bangarorin biyu zuwa wani taron da shugabannin jam’iyyar suka halarta a Kano.

“Mai girma Gwamna Abdullahi Ganduje, ya sasanta Murtala Sule Garo da ni.
“Yayi kiranmu zuwa wani taron sasanci. Taron ya samu halartar Nasiru Koki da shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas. Taron ya fara wurin karfe 11 na dare har zuwa 4 asuban yau Litinin.

“Mun sake duba abinda ya hada mu kuma mun bai wa juna hakuri. Gwamnan ya fada mana kalamai tausasa. Ya bayyanawa kowannenmu inda bai kyauta ba. Ya bamu shawarar iyaye kuma yace ya dauka dukkanmu biyu a matsayin ‘ya’yansa.”

– Doguwa ya bayyana.

A don haka ya bayyana cewa ya bar wannan lamarin rikicin kuma zai mayar da hankali wurin ganin nasarar APC a Kano da Najeriya.

“Ni na bar lamarin. Zan cigaba da goyon baya tare da tabbatar da nasarar APC a 2023. Zan cigaba da goyon bayan Gawuna da Garo, Tinubu da Shettima da kuma APC a dukkan mataki a 2023.”
– Ya bayyana.

Doguwa ya kara da bayyana cewa ya yafewa Garo da dukkan ‘yan jam’iyyar da suka saba masa kuma yana kira garesu da su yafe masa.

Ya kara da kira ga ‘yan jihar Kano da su yafe masa da kuma magoya bayansa na APC a Kano kan abinda ya faru a jam’iyyar.

Leave a Comment