Hassada yan Niger sukewa yan Film da mawakan su ya kamata su farka

Wannan Maganar idan aka kalleta babu a inda irin haka bata faruwa sai dai na wani wajen yafi na wani amma kuma idan aka tsaya aka kalli abinda idon basira zakuga abune wanda addini ma ya hana hakan amma wasu kuwa basu da wani aiki sai wannan yana da kyau malamai su farka su cigaba da wa’azantar da jama’a kan haka

Wata mata a wannan manhajar ta tiktok itace wacce ta fadi haka kuma maganar tata tazo a kan gaba domin hakan kamar tunasarwa ce indai har za’a cire son rai a dubi abin wallahi magana ce mai ma’ana kuma mai mahimmanci

Amma duk da haka wasu sai sunyi magana sun nuna kamar hakan kuskure ko kuma itace wacce take abinda ta fada amma kuma ko kadan ba haka bane ita gaskiya ko daga wajen wa ta fito karba ake Allah dai ya bamu ikon jin gaskiya sannan kuma ya bamu ikon Binta.

Tace a kasar ta Niger kowa bashi da wani aiki sai kushe yan Film koda kuwa abokin sane ya samu damar shiga wannan harkar to daga wannan ranar ya zama abokin gwanarsa kuma ba komai ne yake janyo haka ba illa Hassada da bakin ciki da suke damun mutane

Leave a Comment