Innalillahi An Yi Asarar Rayuka Yayin da Rikici Ya Kaure Tsakanin Sojoji da Wasu Matasa

Imo – Mutane da-dama ake zargin sun hallaka yayin da matasan Izombe a garin Oguta a jihar Imo, suka yi rigima da dakarun sojojin Najeriya.

The Nation ta kawo rahoto a safiyar Talata, 8 ga watan Nuwamba 2022 cewa mutane sun tafi barzahu a sanadiyyar karon-battar da aka yi a Jihar.

Yayin da dakarun bataliya ta 34 Artillery da ke Obinze ta je karamar hukumar Oguta domin maganin masu tada zaune tsaye, sai rikici ya kaure.

Kisan wani direban kamfanin Dangote da ake zargin matasan garin sun yi, ya jawo aka aika rundunar sojoji zuwa yankin domin kawo zaman lafiya.

An kashe Direban Dangote

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi wa direban motar Dangote kisan gilla, don haka jami’an sojoji suka tsaurara matakai domin a kare rayuka.

Daily Trust tace an ji harbe-harbe a lokacin da matasan suka kai wa motocin jami’an sojojin hari. Wani mazaunin yankin yace sojoji ne suka fara harbi.

Majiyar tace daga shiga garin ne jami’an sojoji suka shiga harba bindigogi babu gaira-babu dalili, an zargi jami’an tsaron da yi wa garin Oguta kutse.

…Ba haka abin yake ba – Sojoji

Da aka tuntubi shugaban bataliyar sojojin kasan, Kyaftin Joseph Akubo ya shaidawa jaridar Tribune cewa ba jami’an tsaron suka fara buda wuta ba.

Kyaftin Joseph Akubo yace matasan ne suka aukawa sojojin da aka tura rangadi a sakamakon ta’adin da aka samu labarin ana fama da shi a yankin.

Babban jami’in bai iya bayyana adadin mutanen da aka rasa ko aka yi wa rauni ba, ya tabbatar da cewa har zuwa lokacin matasan na kai wa sojoji hari.

Ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan takaddama a yakin kudu maso gabasin Najeriya ba, inda ‘yan IPOB suka yi karfi a wasu jihohi.

Leave a Comment