Innalillahi Wani Mahaifi Ya Kashe Diyarsa Yar Shekara 20 Saboda Ta Kama Masa Mazantaka

Akwa Ibom – Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama wani Magidanci, Sunday Etukudo, bisa zargin halaka ɗiyarsa Ofonmbuk Sunday, yar shekara 20 a kauyen Omum Unyiam, ƙaramar hukumar Etim Ekpo.

Channels tv ta ruwaito cewa mutumin yayi ajalin matashiyar budurwar ɗiyar tasa ne bayan wani saɓani y ashiga tsakaninsu a cikin iyali.

Yacce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa mamaciyar ta damƙe masa mazantaka yayin da faɗa ya kaure tsakaninsu, hakan yasa ya mangareta da Sanda ta baje ƙasa.

Ganin haka, magidancin ya ɓinne gawar ɗiyar a harabar gidansa dake kauyen Omum Unyiam, da nufin ɓoye laifinsa amma yan sanda sun tono gawar kuma sun ɗauketa domin gwaji.

Mista Macdon yace:

“Bisa bayanan da muka tattara, a ranar 9 ga watan Oktoba, 2022, da karfe 7:10 na dare, wani Sunday Etukudo ya kashe tare da binne diyarsa a harabar gidansa da ke ƙauyen Omum Unyiam.”
“Mutumin yace wani saɓani ne ya taso a cikin gida har ta kai ga faɗa kuma ɗiyar ta damƙe masa mazantaka, shi kuma ya yi amfani da sanda ya mangareta.”
“Sakamakon haka ne ta rasa rayuwarta kuma ya yanke shawarin ya ɓinne ta a harabar gidan domin lulluɓe wannan ɗanyen aikin da ya aikata.”

Wane mataki hukumar zata ɗauka?

 

Da yake tsokaci kan batun, kwamishinan yan sandan Akwa Ibom, Olatoye Durosinmi, ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan Kes din. A cewara zasu gurfanar da wanda ake zargi nan ba da jimawa ba.

Ya kuma gargaɗi mutane su guji ɗaukar doka a hannu sannan ya rokesu da su kai rahoton duk wani saɓani wurin hukumar yan sanda

Leave a Comment