Kotu Ta Bada Umarnin a Yi wa wasu ‘Yan TikTok Bulala 20 Kan Zagin Ganduje

Kano – Wata kotun majistare dake zama a jihar Kano tayi umarnin ba wa Uniquepikin da Nazifi Muhammad, bulala ashirin kan batawa Gwamna Abdullahi Ganduje suna a wani bidiyon TikTok.

Masu bidiyon barkwancin an kama su cikin kwanakin nan tare da gurfanar dasu a gaban kot bayan wani bidiyonsu ya yadu suna alakanta Ganduje da rashawa.

An kai su gaban alkali kan laifuka biyu da ake zarginsu da shi.

A yayin zaman kotun, Alkali Aminu Gabari yayi umarnin yi wa kowanne daga cikinsu bulala 20 sannan su share farfajiyar kotu na tsawon kwanaki 30z.

Kotun ta umarci kowanne daga cikin masu wasannin barkwancin da ya biya N10,000.

A bidiyon, masu wasan barkwancin sun ayyana Ganduje da ‘Dan siyasa mai cin rashawa wanda ke siyar da kowanne fili da ya ci karo da shi na jihar.

“Wannan babi ne dake bayani kan Ganduje. Kuma wanene Gandujen nan? Shi ne mijin shahararriyar mata kuma uban Balarabe. Asalinsa ‘Dan jihar Kano ne. Halayen Ganduje sune kamar Haka: Gwamna ne dake son barci.”
– Suka ce.

“Amma ya zama abun zargi a idanun jama’ar Kano. Idan za a bayyana kadan daga cikin halayensa da baiwoyinsa, in har ya ga fili a Kano toh tabbas sai ya kwashi rabonsa. Domin karin bayani kan hakan, ko dai ya siya ko kuma ya killace, a karshe dai wani abun tambaya sai ya taso.”

Leave a Comment