Ni Ba Musulmi Bane, Ba Kirista Bane Kuma Bana Bautar Gunki, Soyinka

Fitaccen marubucin nan na Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa shi ba Kirista bane, ba Musulmi ba kuma ba dan addinin gargajiya bane.

PM News ta rahoto cewa Soyinka ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba, a wajen gabatar da wasu kasidunsa.

Soyinka na amsa wata tambaya da aka yi masa game da addininsa ne a zauren tambaya da amsoshinsu.

Babban marubuci ya ce babu ruwansa da addinin kiristanci, Musulunci ko bautar gumaka wato addinin gargajiya, sannan cewa bai taba ji a ransa akwai bukatar ya bautawa wani ba.

Ya ce shi babu wani abun bauta da yake bautawa kuma yana kallon gumaka a matsayin zahirin gaskiya, don haka, sune abokan tafiyarsa a duk lokacin da yayi balaguro imma a zahiri ko a badini

Leave a Comment