Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

Fitacciyar jarumar fina-finai Raham Sadau, tayi martani ga matashin da yayi ikirarin cewa zai iya siyar da gonar gadonsa saboda ita.

Jarumar ta wallafa wani tsulelen hotonta ne a kafar yada zumuntar zamani ta Facebook inda tayi shigar matar aure.

Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

Duk da dai hoton an dauke shi ne yayin da ake daukar shiri mai dogon zango mai suna Matar Aure wanda gidan talabijin na Arewa24 ke haskawa, jarumar ta fito tsaf tamkar matar auren.

Wallafa hoton a shafinta Na Facebook babu dadewa masoyanta suka yi mata caa ida suke ta tsokaci tare da tofa albarkacin bakinsu.

A tsokacin Ibrahim Abdullahi Sulaiman Shugaba, yace:

”A kan ki zan iya siyar da gonar gadonmu kwarankwatsa.”
Sai dai jarumar bata yi kasa a guiwa ba inda taje tayi masa martani da cewa:

“Ka bar mana mu yi noma tare…”
Ba wannan bane karo na farko da jarumar ke saka hotuna a kafafen sada zumuntar zamani ba har a yi mata tsokaci, sai dai bata cika kula masu yi mata tsokacin ba sakamakon zagi da sukar da take sha.

Leave a Comment