JARUMIN barkwanci a Kannywood, Aliyu Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork ko kuma Maɗagwal, ya bayyana cewa akwai muhimmin saƙo da jagoran Shi’a a Nijeriya, Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky, ya ba shi domin ya isar ga ‘yan fim ɗin Hausa.

Amma ya ƙaryata masu cewa ya zama ɗan Shi’a, wai don haka ne ma ya kai ziyara ga shahararren malamin a gidan sa da ke Abuja.
Da ya ke zantawa da mujallar Fim, Ali Artwork ya ce, “Masu yaɗa cewa wai na karɓi Shi’a ƙarya su ke yi. Duk wanda ya san ni, ya san cewa a kowace ɗariƙa ina da mutane. Da ma na saba ziyartar malamai tun ba yanzu ba, irin malaman Izala, Tijjaniyya, Ƙadiriyya da duk wani malami, duba da yanayin sana’a ta na nishaɗantarwa, kowane ɓangare na al’umma su na ji, kuma su na kallo.