Tofa shiga kagani fada ya barke tsakanin yan ta adda da yan Al’qa’ida ana ruwan bala’i anan

Wata sabuwa ku karan ta tahotanni daga Mali na cewa kazamin fada ya ɓarke a gabashin ƙasar tsakanin ƙungiyoyin masu iƙirarrin Jihadi da ke adawa da juna.

 

Rahotanni na cewa, tsagin ƙungiyar Al Qaeda da ke gudanar da harkokinsa a wasu ƙasashen yankin Sahel na arewaci da ƙasashen Yamma ya fitar da sanarwa inda ya ce mayaƙansa sun shafe watanni suna ta fafatawa da ƴan tawayen IS.

Al Qaeda ta ce ta kashe fiye da masu tsattsauran ra’ayi ɗari kamar yadda ta bayyana mayaƙan IS,
Ta ce faɗan ya faru ne kusa da Tessit da ke yankin Menaka, duka ɓangarorin biyu sun wallafa bidiyon rikicin a shafukan sada zumunta.

Rundunar sojin Mali dai ta shafe tsawon shekaru tana yaƙar ƙungiyoyi masu iƙirarin Jihadi da a yanzu take samun tallafi daga ƙungiyar Wagner ta sojojin haya daga Rasha.

Leave a Comment