Tofa yadda fati tasha dakar a hannun Hadiza gabon saboda yi mata wasu tambayoyi abun naga Kullum gaba yake.
Tun sanda jaruma Hadiza gabon ta bude wannan toom din bata take gayyatar manyan Mutane daga cikin harda jaruman kannywood maza da mata domin tattauna wasu muhimman abubuwa akai wanda suka shigewa al’umma ido cikin ikon Allah yau kuma ta gayyaci fati washa
A yanzu fati washa tana shan sharafinta tun bayanda ta bayyana acikin shirin labarina shikkenan likafarta ta kara sama kuma mutane suka kara saninta wanda ita kansa tana farin ciki da kuma alfahari da wannan shirin
Akwai tambayoyi masu jan hankali wanda akayi mata wanda daga ciki harda cewa shin kodai itace tayi bita da kulli dan gani an cire tsohuwar sumayya daga wannan shirin dan ta mayar da gurbin ta wanda ta amsa da cewa ko kadan ba ita bace hasalima itace wacce ya yanke hakan da kanta.
https://youtu.be/jhHk5lN5gDQ
Kowa yasan yadda wannan jarumar take da yawan fara’a ga kowa hakan yasa shirin yayiwa mutane dadi sosai saboda yadda aka dinga Wada da kuma da dariya tsakaninta da mai gabatar da shirin wato Hadiza gabon.