Kungiyar yan bijilanti da ke da goyon bayan gwamnati sun kai harin kwantan bauna kan mayakan kungiyar ta’addanci a yankin karamar hukumar Konguno ta jihar Borno.
Kamar yadda gidan talbijin na AIT ya rahoto, yan sa-kan sun yi nasarar murkushe mayakan Boko Haram uku a harin.
An tattaro cewa yan bijilanti din sun kama tare da bindige biyu daga cikin yan bindigar a hanyar su ta zuwa karban wasu kudade na kudin fansa daga iyalan wani mutum da suka yi garkuwa da shi a yammacin ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba.
Zagazola Makama ya samo daga majiya abun dogaro cewa an tsinci gawar daya daga cikin yan ta’addan da ya tsere da raunuka daga bisani.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kuma kwato makamai da babur a daga wajen masu tayar da kayar bayan.